Isa ga babban shafi
Rwanda

‘Yan tawayen FDLR sun ki aje makamai-MDD

Shugaban aikin samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin duniya Herve Ladsous yace akasarin ‘Yan Tawayen FDLR na kasar Rwanda sun ki aje makamansu kafin cikar wa’adin watan Janairu da aka gindaya, yana mai cewa ya zama wajibi a yi amfani da karfi wajen murkushesu. Ladsous ya shaidawa majalisar cewar ko a cikin yan kwanakin nan sojojin majalisar sun fafata da sauran ‘yan tawayen ADF da ke kasar Uganda wadanda ke kai hare hare gabashin Congo.

'Yan tawayen  FDLR na Rwanda
'Yan tawayen FDLR na Rwanda AFP/ Lionel Healing
Talla

Kungiyar FDLR da ta kunshi tsoffin sojoji da mayakan Hutu da suka aikata kisan kare dangin da aka yi a Rwanda a shekarar 1994 sun sanar da shirin aje makaman su a watan Afrilu..
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.