Mata ne suka kai hare hare a Kano
‘Yan Sandan Jihar Kano a Najeriya sun tabbatar da cewa wasu mata guda biyu suka kai harin bama bamai a kasuwar Kantin Kwari a jiya Talata. Wannan na faruwa duka mako guda da aka kai wani kazamin hari a cikin babban Masallacin tsakiyar garin na Kano.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane shida inda wasu bakwai ke kwance a asibiti sanadiyar hare haren kunar bakin wake da ‘yan mata biyu suka kai.
Kungiyar agaji ta Red Cross tace mutane 10 suka dauka zuwa asibiti wadanda suka samu raunuka a sakamakon hare haren.
Shedun gani da ido sun tabbatarwa Wakilin RFI Hausa Abubakar Isa Dandago cewa Mata ne suka tayar da bom din da misalin karfe 3 na rana, lokacin da ‘Yan kasuwa ke cikin hada-hadar kasuwanci a Kantin Kwari.
Rahoton harin Kantin Kware a Kano
Kwamishin ‘Yan Sandan Kano Adenrele Shinaba yace Mata ne suka kai hare haren sanye da Hijabi.
Bama baman dai sun tashi ne a inda ake ajiye ababen hawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu