Isa ga babban shafi
Nijeriya

Sama da mutane 120 ne suka mutu a harin birnin Kano

Rahotanni daga birnin Kano a arewacin Najeriya, sun ce a halin yanzu yawan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon fashewar bama-bamai a wannan juma’a sun kai mutane 120, yayin da wasu akalla 270 suka samu raunuka.

Sur le lieu du triple attentat à la bombe contre la Grande Mosquée de Kano, dans le nord du Nigeria, le 28 novembre 2014.
Sur le lieu du triple attentat à la bombe contre la Grande Mosquée de Kano, dans le nord du Nigeria, le 28 novembre 2014. REUTERS/Stringer
Talla

Ma’aikatan agajin sun tabbatar da wannan adadi, yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan ceto ga wadanda suka samu raunuka a wannan hari da aka kai a masallacin juma’a da ke kofar gidan mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi na biyu.

An dai kai harin ne a daidai lokacin da dubban musulmi suka taru domin gudanar da sallar juma’a, kuma an ruwaita fashewar bama-bamai akalla 3 jere da juna a masallacin.

Har ila yau rahotanni sun ce bayan tashin bama-baman, wasu mutane da aka ce yawansu ya haura goma, sun ci gaba da yin harbi irin na mai kan uwa da wabi, lamarin da ya kara firgita jama’ar da ke kokarin tsira da rayukansu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.