Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

Likitan Mata a Congo ya karbi lambar yabo ta Sakharov

Wani likita dan Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo mai suna Dr Denis Mukwege, ya samu kyautar yabo ta Sakharov wadda Majalisar Tarayyar Turai da ke birnin Strasbourg ke bai wa wanda ya taka rawar azo a gani a wani bangaren na ci gaban rayuwa.

Martin Schulz, yana mika kyautar lambar yabo ta Sakhraov ga Mukwege
Martin Schulz, yana mika kyautar lambar yabo ta Sakhraov ga Mukwege REUTERS/Vincent Kessler
Talla

Dr Denis wanda kwararren likita ne a game da cututukan da suka shafi mata, yana aiki ne a wani asibiti da ke garin Panzi na lardin Kudancin Kivu yankin da ake da dimbin ‘yan gudun hijira a Jamhuriyar dimokuradiyyar Congo.

Likitan dai na daga cikin jami’an kiwon lafiyar da suka taka gagarumar rawa wajen kula da dimbin mata da suka fuskanci fyade a yankin, kuma wannan yana a matsayin dalilin da ya sa Majalisar ta Tarayyar Turai ta ba shi wannan tukuici.

Shugaban Majalisar Martin Schulz, wanda ya mika kyautar yabon ga likitan mai shekaru 59 a duniya, ya bayyana cewa Dr Denis Mukwege, ya taimaka wajen ceto rayukan mata da dama da suka fuskancin fyade da kuma sauran nau’o’I na azabtarwa daga ‘yan tawaye a tsawon shekaru 16 da ya share yana aiki a yankin na Kivu.

A bara  an bayar da wannan kyauta ne mai taken ‘’Sakharov’’ ga ‘yar gwagwarmaya a Pakistan Malala Yusufzai, kuma daga cikin wadanda suka taba samun kyautar daga shekarar 1988 zuwa yau sun hada da Nelson Mandela da kuma Aung San Suu Kyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.