Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

Jam’iyyar Gbagbo tace shi ne dan takararta

Jam’iyyar adawa ta FPI a kasar Cote d’Ivoire ta bayyana tsohon shugaban kasar da ke tsare a kotun Duniya Laurent Gbagbo a matsayin wanda zai tsaya mata takara a zaben shugabancin kasar na shekara mai zuwa.  A sanarwar da ta fitar a yammacin jiya, jam’iyyar ta ce Gbagbo na daga cikin ‘yayan jam’iyyar da wani kwamitin da aka kafa ya wanke domin tsayawa a zaben na watan yulin shekara mai zuwa.

Laurent Gbagbo, Tsohon Shugaban Cote d'Voire
Laurent Gbagbo, Tsohon Shugaban Cote d'Voire AFP PHOTO/ POOL/ MICHAEL KOOREN
Talla

Haka kuma Jam’iyyar ta tantance abokin takararsa Pascal Affi N’Guessan, shugaban Jam’iyyar na yanzu. Amma N’Guessan ya bukaci a cire sunan Gbagbo saboda halin da yake ciki.

Jam’iyyar na shirin gudanar da babban taronta a tsakiyar watan Disemba.

Gbagbo yana fuskantar tuhume-tuhume guda hudu a kotun hukunta manyan laifuka ta ICC da suka hada da keta hakkin bil’adama a lokacin da ya ki amincewa ya mika mulki ga Allassane Ouattara bayan ya sha kaye a zaben 2010.
Mutane akalla 3,000 ska mutu a rikicin.

A ranar bakwai ga watan Yuli ne Gbagbo zai gurfana gaban kotun kafin gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Cote d’Ivoire a watan Octoban 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.