Isa ga babban shafi
Nijar

An saki mutane 16 da ake zarginsu da cinikin Jirirai a Nijar

Hukumomin kasar Nijar sun yi wa mutane 16 sakin talala daga cikin mutanen da ake zarginsu da cinikin jirajirai. Amma ba tare da sakin matar tsohon shugaban Majalisa Hama Amadou ba wanda ya tsere zuwa Faransa.

Minista Abdou Labo
Minista Abdou Labo tamtaminfo
Talla

Mai gabatar da kara Ibrahim Boubakar Zakaria yace sakin mutanen baya da alaka da dambarwar siyasar Majalisa a kasar.

Ministan ayyukan noma Abdou Labou da matarsa suna cikin wadanda aka saki.

Lauyan da ke kare matar Hama Amadou yace sun shigar da bukatar a bayar da belinta.

A watan Yuni ne aka tuhumi mutanen 17 da mallakar Jirirai ba bisa ka ka’ida ba, lamarin day a shafi manyan ‘Yan siyasar Nijar.

A cikin makon nan ne Majalisar dokokin kasar Jamhuriyyar Nijar ta zabi Amadou Salifou a matsayin sabon Kakakinta don maye gurbin Hama Amadou wanda ya tsere zuwa Faransa saboda badakalar mallakar ‘yaya ba kan ka’ida ba.

Hama Amadou babban mai adawa da shugaba Issoufou ya fice Nijar ne a watan Agusta bayan majalisa ta amince a kaddamar da bincike akansa game da badakalar mallakar ‘ya'ya ba bisa ka’ida ba da aka yi fataucinsu daga Najeriya zuwa Cotonou.

Hama Amadou ya ce zargin da a ke ma sa yarfe ne na siyasa, kuma ya ce zai iya kare kansa a gaban mahukuntan Faransa.

Masu sharhi dai suna ganin Matan ‘Yan siyasar ne suka tursasa ma su sayen Jariran saboda matsalar rashin haihuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.