Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Mugabe ya sauya tsarin Zanu PF

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya yi wa kundin jam’iyarsa ta Zanu PF gyaran fuska al’amarin da yanzu haka ya ba shi ikon zaben mataimaka. Kafin wannan gyaran, mambobin yankunan kasar goma ne ke da alhakin zaben mataimaka.

Robert Mugabe tare da matarsa Grace  à Harare
Robert Mugabe tare da matarsa Grace à Harare Reuters/Philimon Bulawayo
Talla

Wannan mataki da jama’iyar ta Zanu PF ta dauka na zuwa ne bayan gudanar da wani zama na gaggawa kafin jam’iyar ta bayyana wa al’ummar kasar sakamakon.

Wannan damar shi zai ba wa Mugabe karfin ikon zabar mataimakansa tare da rike shugabancin jam’iyar da ya dade yana rike da ita yanzu sama da shekaru 28.

Joyce Mujuru mataimakiyar shugaba Mugabe dai ta sami kanta cikin tsaka-mai-wuya inda a farko ake zarginta da son maye gurbin Mugabe al’amarin da ya kai ga tsige wasu magoya bayanta da ke rike da manyan mukamai a gwamnati

Shugaba Robert Mugabe mai shekaru 90 da ya rike mulkin kasar ta Zimbabwe tun bayan samun ‘yanci kasar daga Turawan Birtaniya ya rike mulkin kasar har tsawon shekaru 34 abinda ya sa ya kasance shugaba a Nahiyar Africa da ya fi kowanne shugaba dadewa a mulki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.