Isa ga babban shafi
Najeriya

Jami'an tsaron Najeriya sun abkawa Ofishin APC a Lagos

Jami’an tsaro sun abka wa wani Ofishin Jam’iyyar adawa ta APC a garin Lagos inda suka cafke Ma’aikatan Jam’iyyar da kuma kwace takardu masu muhimmaci tare da lalata kwamfutoci da dama a Ofishin, kamar yadda Kakakin Jam’iyyar Lai Muhammed ya tabbatar.

Tambarin Jami'ar adawa ta APC a Najeriya
Tambarin Jami'ar adawa ta APC a Najeriya
Talla

Jam'iyyar APC tace Ma'aikatanta 28 Jami'an tsaro suka cafke a samamen da suka kai a Ofishinta da ke Lagos tare lalata kwamfutoci da dama.

Lai Muhammad ya danganta al'amarin a matsayin abu mafi muni da ya taba gani a siyasar Najeriya.

APC ta yi kira a kafa kwamiti na musamman domin binciken wadanda suke da hannu ga al'marin.

Wannan na zuwa ne bayan al’amarin da ya faru a Majalisar kasar, inda Jami’an tsaro suka yi amfani da hayaki mai sa kwalla domin haramtawa Kakakin Majalisar Wakilai Aminu Waziri Tambuwal shiga zauren majalisa bayan ya canza sheka zuwa Jam’iyyar adawa ta APC.

Jami’an tsaron farin kaya sun zargi Jam’iyyar adawar da satar bayanan hukumar Zabe don samun galaba a babban zaben da za a gudanar a 2015.

Da ya ke mayar da martani, Kakakin Jam'iyyar Lai Muhammed yace Ofishin cibiya ce da ke kula da ayyukan mambobin Jam'iyyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.