An rantsar da Kafando a matsayin shugaban riko
Michel Kafando ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban riko na kasar Burkina Faso, a daidai lokacin da kasashen duniya ke ci gaba da jinjina wa al’ummar kasar dangane da cim ma jituwa kan wanda zai jagoranci kasar domin dawo da ita kan turbar dimokuradiyya.
Wallafawa ranar:
A yau Talata ne aka rantsar da Kafando domin jagorantar kasar har zuwa a gudanar da sabon zaben shugaban kasa bayan hambarar da gwamnatin Blaise Compaore.
Kafin gudanar da bikin rantsuwar, an karrama Kanal Isaac Zida shugaban Soja wanda ya amince ya mika mulki ga farar hula.
A ranar Juma’a ne Kafando zai karbi ragamar tafiyar da Burkina Faso daga hannun Kanala Zida.
Sauyin gwamnati da aka samu a Burkina Faso na zuwa kafin cikar wa’adin kungiyar Tarayyar Afrika, bayan gargadin kakabawa kasar Takunkubi idan har sojoji ba su mika mulki ga Farar hula ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu