‘Yan sandan Kenya sun wa Masallatai dirar-mikiya
Jami’an tsaron Kenya sun kaddamar da samame a wasu Masallatai da ke birnin Mombasa domin farautar Mayakan kungiyar al Shabaab. ‘Yan sandan sun kashe mutum guda a samamen da suka kaddamar da sanyin safiyar Litinin.
Wallafawa ranar:
Jami’an tsaron sun kaddamar da samamen ne a Masallacin Musa da Sakina da ke birnin Mombasa, bayan sun samu labarin kungiyar al Shabaab na shirin kai hari a cikin kasar.
‘Yan sandan sun cafke mutane da dama, kamar yadda shugabansu Geoffrey Mayek ya tabbatar.
Tuni dai kasashen Turai suka bukaci mutanensu su kauracewa tafiya birnin Mombasa saboda barazanar tsaro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu