Isa ga babban shafi
DRC Congo

An kawo matakin karshe a shari'ar da ake yiwa Jean Pierre Bemba

An kawo mataki na karshe na shari’ar da ake wa tsohon jagoran ‘yan tawayen MLC, na Jamhuriyar Demokradiyar Congo Jean Pierre Bemba a kotun hukunta mayan laifukan ta duniya ICC. Ana zargin madugun ‘yan tawayen da aikata kisa da kuma fyade a kasar.Bayan saureren karar tsohon jagoran ‘yan tawayen MLC Jean Pierre Bemba, Alkalin kotun hukunta mayan laifuka ta ICC ya sanar da cewa kotun zata yanke hunkuci kan tuhumar da ake yi masa na halakan dubun dubatar fararen hula, tareda aikata wasu laifuka da suka hada da fyade, lalata dukiyoyin jama’a da sauren su daga shekara ta 2002 zuwa 2003.Bincike ya nuna cewa Bemba, da dakarun sa suka Harbe mutane 1500, ya isa kasar Afrika ta tsakiya, domin kai dauki ga tsohon Shugaban kasar Ange Felix Patassse, da Francois Bozize ke yukunri yiwa juyin mulkin a wancan lokacin.Binciken ya gano cewa a lokacin ne dakarun Jean Pierre Bemba suka galazawa al’uma fararen hula, tuhumar da madugun ‘yan tawayen yayi watsi da ita.Tsohon mai kare Jean Pierre Bemba Aime Kilolo, ya bayanawa kotun cewa tuhumar da ake yiwa Bemba da cewa shine ya jagoranci dakarun zuwa Afrika ta tsakiya, zargi ne mara tushe.Ya kara dacewa dakarun MLC na Jamhuriyar demokradiyar Congo sun sha baban da na Afrika ta tsakiya.Kotun ta gayaci sama da mutane 3,000 a matsayi shaidu, don bayar da bahasi.An dai kama Jean Pierre Bemba mai shekaru 52 a duniya tun shekara ta 2008.  

Jean Pierre Bemba, a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta ICC
Jean Pierre Bemba, a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta ICC AFP/Peter Dejong
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.