Isa ga babban shafi

Hukumar lafiya ta duniya ta nada sabuwar shugaba a nahiyar Africa

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, da ke ci gaba da shan suka kan yadda take tafiyar da yaki da cutar Ebola dake ci gaba da yaduwa a yankin yammacin Afrika, ta nada wata sabuwar darakta a nahiyar Afrika. An nada yar kasar Boswana Dr Matshidiso Rebecca Moéti, a matsayin wacce zata kula da ayyukan hukumar a nahiyar ta Africa.Uwargida Moéti, da wakilan kasashe 46 na nahiyar Afrika mambobin hukumar lafiya ta duniya suka zaba, a wani taro da suka gudanar a kasar Jamhuriyar Benin, zata maye gurbin dan kasar Angolar nan ne Luis Gomes Sambo, dake rike da mukamin tun cikin 2005, wanda zai kawo karshen wa’adin aikinsa a farkon shekarar 2015.An yi ta sukar hukumar kan yadda ta yi ta jan kafa wajen daukar matakan dakile yaduwar cutar ta Ebola a nahiyar Afrika, inda tuni ta yi sanadiyar mutuwar mutane kusan dubu 5 a yayinda wasu dubu 15 suka kamu da ita, a kasashe 8 dake yanki yammacin Afrika mafi yawa daga cikinsu kuma yan kasashen Libaria Saliyo da Guine ne.Mme Moéti ta dauki alkawalin cewa, zata yi aiki wurjanjan wajen kyautata yaki da cutar ta Ebola a filin dagar kasashe uku da cutar ta Ebola ke ci gaba da ta’annati a cikiA baya dai Mme Moéti, na rike da mukamin mataimakiyar darakatan hukumar lafiya ta duniya a yammacin Afrika ne, kuma yanzu ta bayyana fatan ganin aniyar da ta kudura ta yaki da annobar ta Ebola a kasashen Liberia, Saliyo da ta cimma nasara 

Alamar hukumar lafiya ta duniya, WHO
Alamar hukumar lafiya ta duniya, WHO
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.