Isa ga babban shafi
Najeriya

Kwankwaso ya bayyana aniyarsa ta takarar Shugaban kasa

Gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban kasa karkashin Jam’iyyar APC mai adawa a Najeriya, yayin da kakakin Majalisa Aminu Waziri Tambuwal ya canza sheka zuwa jam’iyyar.

Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso
Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso pointblanknews.
Talla

Kwankwanso shi ne Dan takara na uku a Jam’iyyar APC da ya bayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa a Najeriya bayan Janar Muhammadu Buhari tsohon Shugaban kasa da kuma Alhaji Atiku Abubakar tsohon Mataimakin shugaban kasa.

Kwankwanso ya bayyana aniyarsa ne a taron yakin neman zabensa a birnin Tarayya Abuja, tare da shan alwashin magance matsalar tsaro da cin hanci da rashawa da farfado da tattalin arzikin Najeriya idan har ‘Ya samu amincewar ‘Yan Najeriya a zaben 2015.

Kwankwaso dai yana cikin gwamnonin arewa da ke takun saka da shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda har ya sa suka fice Jam’iyyar PDP mai mulki zuwa APC.

Yanzu babban kalubalen da ke gaban Kwankwaso shi ne samun nasarar zaben fitar da gwani tsakanin shi da manyan ‘Yan takara guda biyu a APC wadanda ke da dimbim mabiya a arewacin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.