Isa ga babban shafi

Faransa ta koka kan yadda ake samun tsaikon tura dakaru zuwa kasar Mali

Faransa ta soki tafiyar hawainiya da ake samu gameda tura Dakarun wanzar da zaman lafiya zuwa yankunan da ake samun tashe tashen hankula a kasar Mali.Cikin wata ira da yayi da gidan Radiyon Faransa, ministan tsaro na kasar Faransa Jean-Vves Le Drian, yayi nuni da cewa tafiyar hawainiyar da ake samu wajen tura Dakarun wanzar da zaman lafiya zuwa yankunan Mali, na sa ana samun ta’adin gaske a yankin.A farkon shekarar bara kasar Faransa ta tura dubban Dakarun ta zuwa Arewacin kasar Mali, tsohuwar kasar data mulka, domin maido da zaman lafiya, bayan kifar da Gwamnati da akayi a lokacin.A bara akayi zabe a kasar, bayan haka kuma MDD ta fito da tsarin maido da zaman lafiya, amma kuma daga bisani wata kungiyar ‘yan tawayen suka bayyana, da ke ikirarin kishin Islama, inda yanzu haka cikin watanni biyu sun kashe sojan Majalisar Dinkin Duniya har guda 20.Ministan waje na Faransa yace arewacin Mali na cikin wani mummunar hali saboda rashin Dakaru da zasu sa idanu kan ta’asar da akeyi a yankin.  

Wasu sojojin Faransa dake aiki a kasar Mali
Wasu sojojin Faransa dake aiki a kasar Mali REUTERS/Joe Penney
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.