Isa ga babban shafi
Najeriya-Kamaru

Sojojin Kamaru sun kashe Mayakan Boko Haram 39

Ma’aikatar tsaro a kasar Kamaru tace sojojin kasar sun kashe Mayakan Boko Haram na Najeriya 39 a wata musayar wuta da suka yi a kusa da kan iyaka tsakanin Kamaru da Najeriya. Tun a ranar Juma’a ne Sojojin Kamaru suka yi musayar wutar da Mayakan na Boko Haram, kuma akwai fararen hula guda hudu da aka kashe kamar yadda Ma’aikatar tsaron Kamaru ta tabbatar.

Motar yaki ta 'Yan Boko Haram a Maiduguri
Motar yaki ta 'Yan Boko Haram a Maiduguri AFP/Tunji Omrin
Talla

Mayakan na Boko Haram sun kai farmaki ne a Kauyen Glawi inda suka kashe mutane hudu cikin wadanda suka yi gudun hijira daga Najeriya.

Ma’aikatar tsaron Kamaru tace Sojojin kasar sun yi nasarar tarwatsa motocin Mayakan Boko Haram da ke dauke da bindigogi da makamai.

Sai dai Ma’aikatar tsaron ba ta bayyana ko akwai Sojan Kamaru da aka kashe ba.

Zuwa yanzu, Sojojin Kamaru sun kashe Mayakan Boko Haram da dama, domin ko a makon jiya Sojojin sun kashe Mayakan su kimanin 107, yayin da Sojojin Kamaru takwas suka mutu.

Wannan ke kara cusa shakku da alamar tambaya ga zukatan ‘Yan Najeriya game da yarjejeniyar tsagaita wuta da Gwamnatin Najeriya ta yi ikirarin ta cim ma da mayakan Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.