Isa ga babban shafi

Oscar Pistorius zai shafe shekaru 5 a gidan yari

Wata kotun kasar Africa ta Kudu ta yanke wa dan tseren guragu Oscar Pistorius hukluncin daurin shekaru 5 a gidan yari, sakamkon samun shi da laifin kashe budurwar shi Reeva Steenkamp, a ranar masoya da ta gabata. Lokacin da take yanke hukunci, alkalin kotu Thokozile Masipa ta bayyana daurin shekaru 5, saboda samun Pistorius mai shekaru 27, da laifin kisan kai.Kotun ta kuma yanke mishi wani hukuncin na daurin shekaru 3, saboda amfani da bindiga ta hanyar da bata dace ba.Hukuncin 2 zasu tafi a lokaci guda ne, da haka Pistorius zai shafe shekaru 5 ne kawai a gidan yari.Masipa tace tana neman daidaito tsakanin hukuncin daya dace da kuma jan kunnne.Alkalin tayi watsi da ikirarin da lauyoyi suka yi, na cewa nakasashshen dan tseren, zai iya shiga yanayi na wahala a gidan yari.A halin da ake ciki kuma, iyalan Steenkamp din sun bayyana farin cikinsu da wannan hukuncin.Mahaifin Steenkamp, mai suna Barry, dake fama da rashi lafiya, yace yana farin ciki da ganin an kawo karshen shari’ar.Shima wani lauyan iyalan na Steenkamp ya bayyana farin ciki da hukuncin da aka yanke wa Pistorius. 

Oscar Pistorius, lokacin da aka tasa keyar shi zuwa gidan yari yau Talata
Oscar Pistorius, lokacin da aka tasa keyar shi zuwa gidan yari yau Talata
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.