Isa ga babban shafi
Madagasca

Hukumomin kasar Madagascar sun tsare tsohon shugaba Ravalomanana

Hukumomin kasar Madagascar sun tsare tsohon shugaban kasar Marc Ravalomanana, daya koma gida, daga gudun hijirar daya je a kasar Africa ta Kudu. Bayan shigar bazata da Mr. Ravalomanana yayi a birnin Antananarivo, sai magoya bayanshi suka taru a kofar gidanshi, inda ya yi musu jawabi.Sai dai sa’a gudu bayan wannan jawabi sai jami’an tsaro suka yi awon gaba da shi, zuwa wani wajen daba a sani ba.Shugaba mai ci Hery Rajaonarimampianina, da bai bayyana inda aka kai Mr Ravalomanana ba, yace ana tsare da tsohon shugaban ne, don kare lafiyar shi, amma ba kama shi aka yi ba.Rajaonarimampianina ya bayyana takaici kan yadda tsohon shugaban kasar ta tsibirin tekun Indiya bai nemi shawara ko izini daga hukumomi ba, kafin komawa kasar ta Madagascar.Mr Ravalomanana ya shafe shekaru 5 yana zaman gudun hijira a kasar Africa ta Kudu, bayan da aka hambarar da gwamnatin shi a shekarar 2009.A shekarar 2010 aka yanke mishi hukuncin daurin rai-da-rai a bayan idon shi, saboda hannu da aka ce yana da shi a mutuwar wasu ‘yan adawa masu zanga zanga su 30, da jami’an tsaro suka kashe a shekarar 2009. 

Lokacin da jami'an tsaro suka kama tsohon shugaban Madagascar Marc Ravalomanana ranar Litinin 13 ga watan Oktoba 2014
Lokacin da jami'an tsaro suka kama tsohon shugaban Madagascar Marc Ravalomanana ranar Litinin 13 ga watan Oktoba 2014 Crédit RIJASOLO / AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.