Isa ga babban shafi
Faransa

An nuna hoton Bafaranshe da aka sace a Aljeriya

Wasu yan bidinga da ba a san ko su waye sun sauce wani dan kasar Faransa mai shekaru 55 a kasar Alajeriya.Al’amarin dake zuwa a dai dai lokacin da Gwamnatin Faransa ta kira yan kasar ta dake kasashen waje da su yi taka cacan . 

Herve Gourdel,bafaranshe da aka sace a Aljeriya
Herve Gourdel,bafaranshe da aka sace a Aljeriya @AFP
Talla

Faransa ta yi gargadi zuwa yan kasar ta dake kasashen waje da su yi taka cacan bayan da kungiyar ISIS ta sanar da cewa zata kadamar da yaki da Faransawa dama Amarukawa a sassa daban daban na Duniyar nan.

Yunkurin wanan kungiya na zuwa ne bawan da kasashen Amaruka da Faransa da sauren kasashe aminai su suka kadamar da yaki a Iraki na gani su kawo karshen kungiyar ta ISIS.

Yan bidingan dai sun yi awan gaba da wanan bafaranshe mai suna Herve Gourdel dan shekaru 55 a garin Tizi Ouzou a daren lahadi.
Tizi Ouzou garin dake da nisan kilometa 110 da babban birni kasar Aljas,
Yayi da a dai wajen rahotani daga yankin na bayyana cewa wanan bafaranshe dan yawon bude ido ne, kuma a halin da ake ciki hukumomin kasar Aljeriya su sanar da gudanar da bicinke dama karfafa matakan tsaro a yankunan kasar..
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.