Shekara daya da kai harin Westgate a Nairobi
Yau lahadi, al’ummar kasar Kenya na juyayin cika shekara daya da harin da ‘yan bindiga suka kai wa cibiyar hada-hadar kasuwa ta Westgate da ke birnin Nairobi inda aka samu asarar rayukan mutane akalla 67 a ranar 21 ga watan satumbar bara.
Wallafawa ranar:
An dai gudanar da addu’o’I a birnin Nairobi, yayin da ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu suka ajiye furanni a wani na musamman da aka gina domin tunawa da mutanen da ‘yan bindiga suka kashe bayan share tsawon kwanaki 4 suna garkuwa da su a cikin wannan kasuwa.
Shugaban rundunar ‘yan sandar kasar ta Kenya David Kimaiyo, ya ce an tsaurara matakan tsaro domin kaucewa yiyuwar kai wa kasar hari a lokacin bukukuwan. An dai bayyana cewa harin na bara, magoya bayan kungiyar Alshebab da ke Somalia ne suka kai shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu