Isa ga babban shafi
Guinea Conakry

Cutar Ebola ta hana bukin ranar ‘yancin Kai a Guinea Conakry

Matsalar yaduwar cutar Ebola a kasar Guinea na ci gaba da tada hankalin hukumomin kasar da a bayan nan suka bayyana shirin dage bukin ranar ‘yancin kan kasar da ya kamata a yi a ranar 2 ga watan Okotoban Bana

ifrc.org
Talla

Wannan dai ya nuna yanda cutar ta yi kamari a kasar da ke zaman dai daga cikin kassahen Afrika da Cutar ta yi kaka-gida.

Fiye da mutane 550 ne aka bayyana cewar Cutar Ebolar ta hallaka a kasar ta Guinea mai fama da tsananin talauci a yankin Afrika ta yamma.

Yanzu haka dai ana ci gaba da bada tallafin kasa-da-kasa daga gwamnatocin kasashen Duniya domin yaki da ita wannan cuta.

Sai dai masu lura da al’amurra na sukar salon taimakon da kasar Amurka ke cewar za ta bayar kan dakile cutar, inda a kwanan nan Amurkar ta bayyana tura Dakarun Soji a kasashen Ebola ta yi kamari domin taimakawa a maimakon aika jami’an kiyon lafiya.

Akasarin mutane dai na kallon hakan a matsayin salon mamayar da Amurka ke son yi a wadannan kasashen da shekaru aru-aru suka kasance karkashin mulkin mallakar kasashen Turai.

Cutar Ebola dai na dai daga cikin Cututtuka masu saukin hallaka mutane.

A kwanannan ma wani dan kasar Britaniya ya bada kan sa domin gwajin maganin cutar ebola, abinda zai bada damar dirka masa cutar a jikin sa domin yin gwaji a Jami’ar Oxford.

Sanarwar tace mutumin na daga cikin mutane 60 da suka bada kansu don gwajin maganin a Britaniya, kamar yadda ake yi a Amurka.

Masu gudanar da binciken na fatar ganin ko maganin zai taimaka wajen gina garkuwar da za ta kare Bil’adama daga kamuwa da cutar nan gaba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.