Isa ga babban shafi
Italiya-Libya

kwale-kwale dauke da bakin haure sun kife a gabar ruwan Malta

Hukumar kula da bakin haure ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane 500 ne suka bace bayan da wasu kananan jiragen ruwa biyu suka yi taho mu gama a gabar ruwan kasar Malta. Lamarin dai ya faru ne kwana daya bayan da hukumomi a kasar Libya suka bayyana cewa wasu bakin haure da dama sun rasa rayukansu a irin wannan hatsari. 

Wasu bakin haure da aka kubutar a teku
Wasu bakin haure da aka kubutar a teku Reuters/Darrin Zammit Lupi
Talla

Sakamakon binciken da hukumomin kasar Malta inda lamarin ya faru suka gudanar ya tabbatar da cewa daya daga cikin jiragen ruwan na dauke da ne mutane akalla 400 a cikinsa, yayin da daya ke dauke da nasa bakin hauren da aka bayyana cewa za su kai 30.
Wadanda suka tsira da rayukansu sun bayyana wa jami’an ceton kasar Italiya cewa, fasinjojin da ke cikin daya jirgin ne suka tunkari daya jirgin bayan da suka fahimci cewa nasu kwale-kwalen na gaf da nutsewa kuma a wannan yanayi ne suka yi karo da juna har ma dukkaninsu suka kife.
Yanzu haka dai jami’an ceto daga kasashen Italiya da kuma Malta na ci gaba da aiki domin gano gawarwaki ko kuma sauran mutanen da ke da sauran numfashi bayan faruwar wannan hatsari.
To sai dai duk da cewa ana samun asarar rayukan jama’a da dama a irin wannan tafiya, amma ko a tsakanin ranakun litinin da kuma talatar da suka wuce sai da jami’an tsaron ruwan Italiya suka ceto wasu bakin haure 2.380 da ke kokarin shiga nahiyar Turai a cikin kananan jiragen ruwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.