Isa ga babban shafi
Najeriya

Jirgin Sojin Najeriya ya bace a Adamawa

Rundunar Sojojin Najeriya tace wani Jirgin Sojinta ya bace tsawon kwanaki biyu a arewa maso gabacin kasar inda Sojojin ke yaki da Mayakan Boko Haram. Sanarwar da Sojojin na Najeriya suka fitar tace jirgin mai suna Alpha Jet da matukansa guda biyu ya bar sansaninsu a garin Yola Jihar Adamawa da misalin karfe 10:45 na safe a ranar Juma’a amma tun lokacin ba a ji duriyarsa ba.

Janar Chris Olukolade, Kakakin rundunar Sojin Najeriya
Janar Chris Olukolade, Kakakin rundunar Sojin Najeriya AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Janar Chris Olukolade yace tun lokacin babu wani labari game da jirgin, amma suna fadada bincike domin gano inda jirgin ya bace.

Sai dai Olukolade bai bayyana cewa ko sun yi amfani da jirgin wajen yaki da mayakan Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.