An dakile yunkurin harin ta’addanci a Uganda
Jami’an tsaro a kasar Uganda sun ce sun yi nasarar gano wani yunkurin harin ta’adanci da Mayakan Al Shabaab suka kulla kai wa a birnin Kampala, a yayin da kuma Amurka ta yi kira ga ‘yan kasarta su nemi mafaka.
Wallafawa ranar:
Rundunar ‘Yan sandan Uganta tace akwai mutanen da suka cafke.
A yau Assabar ne ofishin jekadancin Amurka ya fitar da sanarwar cewa Jami’an tsaron Uganda sun gano mabuyar mayakan Al Shabaab inda suke shirin kai hare hare.
Yanzu haka kuma Uganda ta tsaurara tsaro musamman a filayen jiragen sama da gine ginen gwamnati da sauran wuraren da ake tunanin Mayakan na iya kai hari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu