Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Pistorius bai kashe Budurwarsa da gangan ba

Mai shari’ar da ke sauraren Karar Oscar Pistorius tace ta gano dan tseren gudun guragun ba da gangan ba ne ya kashe Budurwarsa, bayan shafe lokaci mai tsawo ana tabka shari’a a Afrika ta Kudu. Yanzu haka an dage sauraren karar har zuwa gobe Juma’a inda ake sa ran za’a yanke wa Pistorius hukunci.

Oscar Pistorius, dan tseren gudun guragu da ake tuhuma ya bindige Budurwarsa a Afrika ta kudu
Oscar Pistorius, dan tseren gudun guragu da ake tuhuma ya bindige Budurwarsa a Afrika ta kudu REUTERS/Kim Ludbrook/Pool
Talla

A yau Alhamis a zaman kotun Pretoria, Mai shari’a Thokozile Masipa ta yi watsi da tuhumar kisa da ake yi wa dan tseren guragu Oscar Pistorius wanda ake zargi ya kashe budurwasa Reeva Steenkamp a ranar masoya ta Valentine.

Mai shari’ar tace masu gabatar da kara sun kasa gabatar da kwararan hujjoji da zasu tabbatar da Pistorius da gangan ya bindige budurwarsa a cikin gidansa.

Amma kuma kotun ta Pretoria ta dage sauraren karar zuwa gobe Juma’a inda kotun zata tabbatar da ko da gangan ne Pistorius ya kashe budurwarsa kafin yanke ma sa hukunci.

Pistorius na iya fuskantar hukunci mai tsauri idan har kotu ta gamsu da shedun da aka gabatar. Haka kuma kotun na iya wanke shi daga zargin da ake ma sa.

Tuni dai Pistorius ya amsa laifin bindige Reeva amma kuma ya musanta aikata harbin da gangan, yana mai cewa ya yi harbi ne akan tunanin wani ne ya kutsa ma sa a cikin gida.

Masana shari’a a Afrika ta kudu sun yi mamakin yadda kotun ta yi watsi da zargin aikata kisa da ake yi wa Pistorius, bayan shafe lokaci mai tsawo ana tafka shari’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.