Isa ga babban shafi
Najeriya

Mayakan Boko Haram sun kewaye Maiduguri

Kungiyar Dattawan Jihar Borno tace Mayakan Boko Haram sun yi wa birnin Maiduguri Kawanya tare da kira ga Sojoji su daura damar yaki idan ba haka ba Mayakan na shirin karbe ikon babban birnin na Jihar Borno.

Wasu fararen hula da ake kira kato da gora da ke yakar Mayakan Boko Haram  a Jihar Borno
Wasu fararen hula da ake kira kato da gora da ke yakar Mayakan Boko Haram a Jihar Borno REUTERS/Joe Penney
Talla

A cikin sanarwar da suka fitar, Kungiyar Dattawan da ta kunshi tsoffin ma’aikatan gwamnati da Sojoji tace Mayakan Boko Haram sun kewaye Maiduguri, kuma bukatar da suke son cim ma ita ce su karbe ikon garin.

Tuni dai Kungiyar Boko Haram ta ayyana kafa sabuwar daula a Jihar Borno bayan sun karbe Gwoza da Dambuwa da Bama da Gamburu Ngala da Ashigashya da wasu garuruwan Jihar Borno da Yobe da Adamawa da dama.

Dattawan sun ce rabin mutanen Jihar Borno sama da Miliyan hudu suna rayuwa ne yanzu a Maiduguri. Dattawan kuma sun yi kira ga gwamnati ta gaggauta kawo dauki idan ba haka ba za a shiga mawuyacin hali na yunwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.