Isa ga babban shafi
Lesotho

Sojoji sun yi juyin mulki a Lesotho

Sojojin kasar Lesotho sun musanta yin juyin mulki a kasar, kamar yadda kakakin rundunar sojin kasar ya shaidawa wata kafar Telebijin a kasar Afrika ta kudu, duk da Firaministan kasar ya yi ikirarin Sojoji sun hambarar da gwamnati, lamarin da ya sa ya tsere zuwa kasar Afrika ta kudu.

Firaministan Lesotho, Tom Thabane, a wata ziyara da ya kai a birnin  Johannesbourg, a kasar Afrika ta kudu
Firaministan Lesotho, Tom Thabane, a wata ziyara da ya kai a birnin Johannesbourg, a kasar Afrika ta kudu AFP PHOTO / GCIS / ELMOND JIYANE
Talla

Kakakin rundunar Sojin kasar Manjo Ntele Ntoi ya shaidawa kafar Telebijin ta ANN7 cewa Sojoji sun kaddamar da farmaki ne domin karbe makamai daga hannun ‘Yan sanda bayan sun samu labarin ‘Yan sandan suna shirin ba wasu Jam’iyyun siyasa makamai.

Tuni dai Firaministan kasar Tom Thabane ya shaidawa kafar yada labaran Birtaniya cewa Sojoji sun karbe mulki kuma dalilin haka ya sa ya tsere zuwa kasar Afrika ta kudu domin tsira da ransa.

Ministan Wasanni Themselves Maseribane ya shaidawa kamfanin dillaccin labaran Faransa cewa Sojoji sun karbe ikon hedikwatar ‘Yan sanda, yana mai cewa sun ji Kwamandan Sojojin yana neman Firaminista da mataimakinsa.

Ministan yace Sojojin sun karbe ikon kafafafen yada labarai, tare da zargi mataimakin Firaminista Mothetjoa Metsing akan da hannunsa cikin juyin mulkin wanda shi ne jagoran Jam’iyyar LCD da suka shiga kawance aka kafa gwamnati.

Kasar Lesotho dai ta fada rikicin Siyasa ne bayan samun baraka tsakanin Jam'iyyun siyasar kasar da suka kafa gwamnatin hadaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.