Benin
Ebola: Benin ta dage taron lafiya na Afrika
Mahukuntan kasar Benin sun dage taron tattauna batun kiwon lafiya na Ministocin kasashen Afrika da aka shirya gudanarwa a Cotonou, saboda annobar cutar Ebola da ke yin kisa cikin hanzari. An shirya gudanar da taron ne na kwanaki biyar daga ranar 1 ga watan Satumba, amma gwamnatin Benin tace ta dage taron ne bisa shawarin da ta samu daga hukumar lafiya ta duniya WHO.
Wallafawa ranar:
Talla
Rahotanni kuma sun ce an kwashi wani likita baturen Birtaniya zuwa birnin London bayan ya kamu da cutar Ebola a kasar Saliyo domin ci gaba da kula da lafiyarsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu