Isa ga babban shafi
Senegal

Ebola: Senegal ta rufe kan iyaka

Kasar Senegal ta rufe kan iyakokinta da ta ke makwabtaka da wasu kasashen yammacin Afrika domin dakile bazuwar cutar Ebola mai yin kisa shiga kasar. Ma’aikatar cikin gida tace sun rife kan iyakarsu da Guinea saboda cutar Ebola da ta hallaka kimanin mutane 1,350 a Guinea da Liberia da Saliyo da Najeriya.

Wani Allon sanarwa akan Cutar Ebola da Jami'an shige da fice suka kafa a kasar Liberia domin tantance mutane
Wani Allon sanarwa akan Cutar Ebola da Jami'an shige da fice suka kafa a kasar Liberia domin tantance mutane REUTERS/Stringer
Talla

Wannan matakin na zuwa ne bayan Majalisar Dinkin duniya ta aiko da wani kwararren likita David Nabarro zuwa kasashen yammacin Afrika domin yaki da Ebola
Naborro zai kai ziyara biranen Freetown a Saliyo da Conakry a Guinea da kuma Abuja a Najeriya, kafin ya koma Geneva domin gabatar da rahoton bincikensa akan Ebola.

Kasar Afrika ta kudu ta haramtawa ‘Yan kasashen Guinea da Liberia da Saliyo shiga cikin kasarta, Sakamakon barazar cutar Ebola mai saurin yaduwa.

Rahotanni daga Cotonou sun ce Hukumomin Jamhuriyar Benin sun hana wasu jami’an gwamnatin Najeriya sauka a kasar, da suka hada da Ministar kudi Ngozi Okonjo Iweala, a wani taro da suka yi niyyar halarta.

An shirya fara taron ne a yau juma’a don duba yanayin tattalin arziki tsakanin Najeriya da Benin da kuma sauran kashen yammacin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.