Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

‘Yan bindiga sun kona kauyuka a Jamhuriyyar Congo

Wasu yan bindiga sun kai hari tare da kona wasu kauyuka dake gabashin Jamhuriyar Demokradiyar Kongo a makon da ya gabata kamar yadda kungiyar wanzan da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a ci gaba da tashe tashen hankula a yankin.

Mutanen da aka raba da muhallansu a Katanga, kasar Jamhuriyyar congo
Mutanen da aka raba da muhallansu a Katanga, kasar Jamhuriyyar congo DR / Refugees International
Talla

Harin da ‘yan bindigan suka kai karkashin jagorancin shugaban su Mubone Mbuyu wani mataki ne na fansa a cewar kakakin kungiyar ta Majalisar.

‘Yan bindigan sun kona kauyuka a yankin Katanga tsakanin ranakun 10 zuwa 12 na watan Agusta inda suka kashe mutane uku.

Rikici a yankin ya kara wargaza fararen hula inda Majalisar Dinkin Duniya ke cewa mutane dubu 545 suka rasa matsugunninsu wato karin kashi 50 cikin 100 kamar yadda alkaluma suka nuna.

Jamhuriyar Demokradiyar Kongo ta fi kowace kasa yawan kungiyoyin agaji na Majalisar Dinkin Duniya duk da haka kungiyar ‘yan gudun hijra ta Amurka a farkon wannan watan ta nemi Majalisar da ta kara aika jami’an wanzar da zaman lafiya zuwa yankin na Katanga domin kare fararen hula da ke ci gaba da fuskantar wariya daga sauran kabilun yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.