Isa ga babban shafi
Najeriya

Yunkurin tsige gwamna Al-makura ya dauki sabon salo

Yunkunrin da ‘yan Majalisar Dokokin jihar Nasarawa da ke tarayyar Najeriya ke yi na tsige gwamnan jihar Umaru Tanko Al-makura, ya dauki wani sabon salo, bayan da ‘yan majalisar suka yi fatali da kwamitin binciken da babban alkalin alkalan jihar ya kafa.

Gwamna Al-makura na rantsuwa
Gwamna Al-makura na rantsuwa
Talla

Bayan wani zaman da suka yi wajen Lafiya babban birnin jihar, ‘yan majalisar wadanda mafi yawansu ‘yan jam’iyyar PDP ne, sun nemi a sauya mambobin kwamitin, bisa zargin cewa wadanda aka nada ba za su yi adalci ba saboda kasancewarsu magoya bayan Al-makura.

To sai dai jam’iyyar APC, a wata sanarwar mayar da martani da ta fitar a wannan alhamis, ta yi watsi da wannan zargi, inda ta bayyana shi da cewa ba ya da tushe balle makama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.