Isa ga babban shafi
Liberia

Sabbin matakai domin hana yaduwar Ebola

A yayin da annobar cutar Ebola ke ci gaba da hallaka rayukan jama’a a wasu kasashe 3 da ke yankin Yammacin Afrika, mahukuntan kasashen Laberia da Sierra Leone, wadanda cutar ke ci gaba da yi wa illa, sun bayyana daukar wasu jerin tsauraran matakan kiyon lafiya.

Jami'an kiwon lafiya na yaki da cutar Ebola.
Jami'an kiwon lafiya na yaki da cutar Ebola. Photo: Reuters/Tommy Trenchard
Talla

Watanni 7 da bullarta, annobar ta yi sanadiyyar mutuwar saman da mutane 700 a cikinsu kuma har da kasar Guinee Conakry mai makwbtaka da su.

Shugabar kasar Laberiya Uwargida Ellen Johnson Sirleaf a ajiya laraba ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun kasar.

A wannan alhamis kuwa takwaranta na kasar Sierra-léonais Ernest Bai Koroma, ya saka kasar cikin dokar ta baci, kan annobar zazzabin nan Ebola mai haddasa tsiyayar jini a cikin jikin dan adam, da masana kiyon lafiya na duniya suka gagara samun maganinta

Shugaban kasar ta Sierra Leone, Ernest Bai Koroma, wanda ya bayyana soke halartar zaman taron da zai hada nahiyar Afrika da kasar Amurka a mako mai zuwa, a dazu ne ya ayyana daukar wannan mataki na shirin ko takwana, wajen hana ci gaba da yaduwa da cutar ke yi, wace kawo yanzu ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 224 a kasarsa.

matakin taka tsantsan din bai tsaya a kan kasashen dake yankin yammacin Afrika ka dai ba ya shafi wasu kasashen dake wasu kusurwowin Afrika, inda kasashen kenya da Ethiopiya dake da filayen tashi da saukar jiragen sama mafiya girma a nahiyar ta Afrika a yau alhamis sun bayyana daukar karin tsaurara matakan kariya wajen hana shigar kwayar cutar ta Ebola a cikin kasashen nasu
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.