Isa ga babban shafi
Saliyo

Likitan da ke kula da Ebola ya mutu a Saliyo

Babban likitan da ke kula da da fannin kawar da cutar Ebola a kasar Saliyo ya mutu, bayan kamuwa da cutar. Dr Sheikh Umar Khan ya yi suna wajen warkar da mutane kusan 100 da suka kamu da wannan cuta da ke kisan Jama’a a yammacin Afrika.

Sheik Umar Khan, Likitan Saliyo da ya mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola
Sheik Umar Khan, Likitan Saliyo da ya mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola REUTERS/Umaru Fofana
Talla

Umar Khan ya rasu ne a wata babbar asibitin Saliyo da misalin karfe biyu na rana a jiya Talata.

Kafin kamuwa da cutar, Likitan shi ke jagorantar aikin warkar da cutar Ebola a wata asibitin garin Kenama da ke gabas da birnin Freetown.

Alkalumman lafiya a kasar Saliyo sun ce kimanin mutane 489 suka kamu da cutar Ebola a kasar Saliyo, yayin da 159 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.