Kamaru ta kori wasu manyan hafsan Sojinta
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya yi wa wasu manyan sojojin kasar Korar kare daga aiki saboda sakaci har ‘yan kungiyar Boko Haram suka fi karfinsu, har ta kai ga kashe mutane bakwai da sace uwargidan wani kusa a gwamnatin kasar.
Wallafawa ranar:
A Ranar lahadi ne wasu ‘Yan bindiga da ake kyautata zaton Mayakan kungiyar Boko Haram ne na Najeriya suka kai hare hare a garin Kolofata da ke arewacin Kamaru inda suka aikata ta’asa.
‘Yan bindigar sun yi awon gaba da ‘Yan Sanda tare da kashe Sojoji guda hudu.
Ta kafar Radiyon kasar, Gwamnatin Kamaru ta bayar da sanarwar korar Kanal Youssa Gedeon Kwamandan Jandarma a arewa mai nisa da kuma abokin aikinsa Kanal Justice Ngonga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu