Isa ga babban shafi
Ebola

Jirgin Asky ya dakatar da jigila a Liberia da Saliyo

Kamfanin Asky da ke jigila a kasashen yammacin Afrika ya dakatar da jigilar Fasinja a manyan biranen Liberia da Saliyo saboda matsalar cutar Ebola. Wannan kuma na zuwa ne bayan mutuwar wani babban likitan da ke kula da cutar a kasar Saliyo. Tuni mahukuntan Najeriya suka dakatar da jirgin Asky saboda dakile yaduwar Cutar Ebola da ta zama annoba a yammacin Afrika.

Samfurin jiragen ASky da ke jigila a kasashen Afrika
Samfurin jiragen ASky da ke jigila a kasashen Afrika
Talla

Hukumar ta dauki tsauraran matakan sanya kafar wando guda da duk wani kamfanin jirgin sama da ya shigo Najeriya da wani mai dauke da cutar Ebola, bayan shigowar wani dan kasar Liberia da cutar a Najeriya.

Kakakin kula da tashohin jiragen Sama a Najeriya Yakubu Datti yace sun dakatar da jirgin Asky ne saboda ya karya doka. Datti yace sun tanadi Likitoci a tashohin jirage a Lagos domin tantance mutanen da ke shigowa daga kasashen da cutar Ebola ta yi kamari.

Kazalika, Kamfanin Arik na Najeriya yace ya dakatar da jigila zuwa kasashen Liberia da Saliyo saboda cutar Ebola.

Hukumar kwallon Liberia ta haramta gudanar da wasannin kwallon kafa a kasar saboda gujewa yaduwar cutar Ebola. Hukumar tace kwallon kafa wasa ne na cudanya, domin mutane na iya kamuwa da cutar nan take.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.