Isa ga babban shafi
EU

Ebola: Kungiyar Turai ta sake bayar da tallafi

Kungiyar Tarayyar Turai ta ware Kudi kimanin euro Miliyan biyu na tallafi domin dakile yaduwar cutar Ebola da ke kisan Jama’a a yammacin Afrika,  a yayin da ake fargabar cutar na iya yaduwa zuwa Nahiyar Turai. Zuwa yanzu babu wani Bature da ya kamu da cutar amma cutar ta shafi wasu Amurkawa guda biyu.  

Wasu jami'an kiwon lafiya a  kasar Guinea da ke aiki akan cutar Ebola
Wasu jami'an kiwon lafiya a kasar Guinea da ke aiki akan cutar Ebola Photo: Reuters/Tommy Trenchard
Talla

Kungiyar Likitocin Doctors Without Borders ta yi gargadin cewa cutar Ebola yanzu ta zama annoba, domin zata iya yaduwa zuwa kasashe da dama. Domin yaki da cutar ne kuma kungiyar Tarayyar Turai ta amince da wasu karin kudin tallafi sama da euro Miliyan biyu tare da tura kwararru zuwa inda cutar ta yi kamari.

Jiragen sama da dama ne suka dakatar da jigila zuwa Liberia da Saliyo saboda fargabar yaduwar cutar zuwa wasu kasashe, musamman wani mutumin Liberia da ya kai cutar a Najeriya kafin ya mutu a lagos.

Ma’aikatar harakokin wajen Birtaniya tace cutar Ebola barazana ce ga Ingila, yayin da tuni bangaren kula da lafiyar al’umma a Birtaniya ya yi gargadi zuwa ga likitocin kasar su dauki matakai.

Cutar Ebola dai ta kashe mutane 672, cikin su har da likitan Saliyo da ke kula da wadanda suka kamu da cutar Ebola.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.