Isa ga babban shafi
Najeriya

Fashewar bama bamai ta rage armashin bukukuwan sallah a Kano

An kai hare haren kunar bakin wake biyu wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 5, yayin da jami’an tsaro suka ce sun kwance bama bamai a wurare da dama da ke birnin Kano na arewacin Najeriya a lokacin da ake gudanar da bukukuwan sallah a birnin.

Wani harin bam da aka kai a birnin Kano na Najeriya
Wani harin bam da aka kai a birnin Kano na Najeriya REUTERS/Stringer
Talla

Da fari dai wata budurwa ce da ta yi basaja cikin masu sayen man kalanzir ta tada bamb na farko, sai kuma na biyu da shi ma wata ‘yar kunar bakin waken ta tarwatasa kanta a kofar shiga filin baje koli da ke birnin.

Hare haren dai sun jefa jama’a a cikin hali na tsoro da kuma haddasa takaita zirga-zirgar jama’a a daidai lokacin da jama’a ke gudanar da bukukuwan karamar sallah.

Har ila yau hare haren sun rage wa bukukuwan karamar sallar armashi sakamakon yadda aka soke bukukuwan hawan sallah da sarki ke yi kowace shekara a wannan birnin mai dadaddin tarihi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.