Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

MDD ta yi gargadin yiwuwar bala'in yunwa a Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin duniya ta roki masu bayar da tallafi su kara kokari, don kawar da barazanar yunwa da ka iya afkawa kasar Sudan ta Kudu. Ya zuwa yanzu kashi 1 cikin 3 na yankar na fuskantar barazar ta yunwa, bayan da aka shafe wata guda ana gwabaza yaki a kasar da bata dade da ballewa ba, daga Sudan.Hukumar samar da Abinci ta MDD, tace kusan yara kanana ‘yan kasa da shekaru 5, miliyon 1 na fukantar rashin abinci mai gina jiki, kuma dubu 50 zasu iya mutuwa cikin wannan shekarar, idan ba a dauki matakan gaggawa ba. 

Wasu kananan yara a kasar Sudan ta Kudu
Wasu kananan yara a kasar Sudan ta Kudu
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.