Isa ga babban shafi
Algeria-Mali

An gano tarkacen Jirgin Algeria a Mali

Masu gudanar da bincike a game da jirgin saman fasinjar kasar Algeria wanda ya bata dauke da mutane 116 lokacin da ya ke kan hanyar Ouagadougou zuwa Algeria, sun ce an gano tarkacen jirgin inda ya fado a kusa da wani gari mai suna Gossi da ke cikin kasar Mali.

Samfurin Jirgin Air Algerie da ke jigila a Algeria
Samfurin Jirgin Air Algerie da ke jigila a Algeria AFP/FAROUK BATICHE
Talla

Shugaban masu gudanar da bincike kan bacewar wannan jirgi Janar Gilbert Diendiere, ya ce mazauna yankin na Gossi sun hango lokacin da jirgin ke fadowa da misalin karfe 1 da minti 50 da daren shekaran jiya.

Fadar shugaban Faransa, kasar da ke da mutane 51 a cikin jirgin ta tabbatar da wannan labari.

Fadar ta shugaban kasar Faransa ta ce yanzu haka an tura sojojin kasar zuwa yankin da lamarin ya faru, yayin da shugaba Francois Hollande ya sanar da soke kai ziyarar aiki zuwa wasu kasashen yankin tekun India a wannan mako domin nuna alhini ga iyalen wadanda suka rasa rayukansu.

Wani lokaci a yau ne ake sa ran shugaban kasar Mali Ibrahim Boubakar Keita zai ziyarci inda hadarin ya faru, kamar yadda karamin Ministan Faransa mai kula da Faransawa da ke zaune a kasashen ketare zai ziyarci kasar ta Mali da kuma Burkina Faso a yau Juma’a.

Jirgin Air Algerie wanda ya taso daga birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso akan hanyarsa ta zuwa kasar Algeria, ya bace ne a lokacin da ya ke dauke da mutane 116 a cikinsa, kuma mazauna kauyen da jirgin ya fado sun ce sun hango yana cin wuta tun daga sararin samaniya.

Wasu na zargin tangardar Inji ce ta haddasa hadarin, wasu kuwa na danganta hakan da lalacewar yanayi, jirgin ya fadi a yanki da yanzu haka ke fama da ayyukan tawaye a cikin kasar Mali.

Faransa tace ba harbo Jirgin aka yi ba, bisa zargin da ake yi cewa ‘Yan tawayen Mali ne suka harbo Jirgin da suke gudanar da ayyukan ta’addanci a cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.