Isa ga babban shafi
Najeriya-Amurka

Harin Kaduna: Amurka ta nemi a yi bincike

Kasar Amurka ta yi Allah waddai da harin da aka nemi hallaka Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Malamin Addinin Islama da Janar Muhammadu Buhari tsohon shugaban kasa, tare da yin kira ga mahukuntan Najeriya su gaggauta gudanar da bincike.

Ma'aikatan agaji da Jami'an tsaro a inda aka kai harin Kaduna
Ma'aikatan agaji da Jami'an tsaro a inda aka kai harin Kaduna Reuters
Talla

Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Marie Harf ta bukaci hukumomin Najeriya su gudanar da bincike na hakika kan harin, tare da bukatar ‘yan kasar su kaucewa daukar matakan ramako.

Akalla mutane 82 aka tabbatar da mutuwarsu a tawayen hare haren da aka kai a Kaduna, kuma yanzu mahukuntan Jahar sun kafa dokar hana fita ta sa’o’I 24.

Da misalin karfe 12: 30 na rana aka fara kai wa Tawagar Sheikh Dahiru Bauchi bayan ya rufe Tafsirin Al Kur’ani mai girma a watan Azumin Ramadan.

Mutane kimanin 50 Jami’an agaji na Red Cross suka tabbatar da mutuwarsu a hari na biyu da aka kai wa Tawagar Janar muhammadu Buhari tsohon Shugaban Najeriya.

A cikin wata Sanarwa Buhari yace an nemi a kashe shi ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.