Jonathan zai gana da iyayen 'yan matan Chibok a wannan talata
A wannan talata ake sa ran shugaban Tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan zai gana karo na farko da iyayen ‘yan mata sama da 200 da kungiyar Boko Haram ta sace a garin Chibok da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.
Wallafawa ranar:
An dai jima ana yada jitar jitar cewa shugaban zai gana da iyayen ‘yan matan musamman ma bayan da mai fafutukar bunkasa ilimin mata a duniya wato Malala Yusafzai ‘yar kasar Pakistan ta neme shi da ya yi hakan.
Ba a dai san muhimman batutuwan da shugaban zai zanta da iyayen ‘yan matan ba wadanda suka share tsawon kwanaki kusan dari daya a hannun ‘yan kungiyar ta Boko Haram.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu