Isa ga babban shafi
Najeriya

Malaman Makaranta 176 aka kashe a Borno

Gwamnatin Jihar Borno ta ce daga shekara ta 2011 zuwa yau, Malaman makaranta 176 ne aka kashe tare da kona makarantu akalla 900 a a cikin Jihar Borno Kawai. Gwamnan Jahar ne Kashin Shettima ya tabbatar da haka a lokacin da ya ke kaddamar da wani kwamiti kan yadda za a samar da tsaro ga makarantun Jihar.

Gwamnan Jahar Borno Kashim Shettima ya ziyarci wani a Asibitin Maiduguri wanda ya samu rauni a wani harin bom da aka kai a wata kasuwa.
Gwamnan Jahar Borno Kashim Shettima ya ziyarci wani a Asibitin Maiduguri wanda ya samu rauni a wani harin bom da aka kai a wata kasuwa. REUTERS/Stringer
Talla

Kwamiti, yana a karkashin wani shiri ne da Majalisar Dinkin Duniya ke taimakawa domin bunkasa ilimi a karkashin jagorancin tsohon Firaministan Birtaniya Gorden Brown.

Mista Brown ya yi alkalin ware kudi dala Miliyan 10 ga shirin taimakawa makarantu a Najeriya.

Kwamitin kuma zai fara aiki ne a Jahohin Borno da Yobe da Adamawa da ke fama da matsalar tsaro.

Tuni aka rufe wasu makarantu a Borno bayan Mayakan Boko Haram sun sace ‘Yan mata 276 a wata makaranta a garin Chibok. Yanzu ‘yan mata 57 sun gudo daga cikin wadanda aka sace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.