Bukukuwan ranar hadin-kan kasa a Jamhuriyar Nijar
A Jamhuriyar Nijar, yau ana gudanar da bukin ranar hadin-kan kasar, ranar da ta samo asali daga yarjejeniyar zaman lafiya ta farko daka kulla tsakanin ‘yan tawaye da gwamnatin kasar a ranar 24 ga watan Afrilun shekarar 1995.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
An dai kulla yarjejeniyar a lokacin tsohon shugaban kasar marigayi Janar Ibrahim Ba’are Mainasara, wanda tare da shiga tsakanin wasu kasashe masu makotaka da Nijar da suka hada Aljeriya, Chadi, Burkina Faso da kuma Mali aka cimma jituwa da Azbinawa da ke fada da gwamnatin kasar.
Tun a wannan lokaci ne dai ake gudanar da bukukuwa domin kara hada kan al’ummar kasar baki daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu