Isa ga babban shafi
Mali-Faransa

Mayakan MUJAO sun kashe Bafaranshen da suka sace a Mali

Mayakan Jihadi a kasar Mali sun sanar da mutuwar wani Baturen Kasar Faransa da suka sace tun a watan Nuwamba na shekarar 2012 da ake kira Gilberto Rodriguez Leal. A Cikin sanarwar da mayakan MUJAO suka fitar, sun ce sun kashe Bafaranshen ne saboda yakin da suke yi da Faransa.

Gilberto Rodriguez Léal da Mayakan MUJAO suka kashe a Mali.
Gilberto Rodriguez Léal da Mayakan MUJAO suka kashe a Mali. "AFP PHOTO / ALAKHBAR"
Talla

Sai dai babu wani karin haske daga bakin Kakakin Kungiyar Yoro Abdul Salam, wanda ya tabbatar da mutuwar Bafaranshen.

Tuni Mayakan na MUJAO suka aika wa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa AFP da sakon gargadin kisan Bafaranshe a bidiyo ta wayar salula.

A cikin Jawabinsa bayan samun labarin Mutuwar Bafaranshen, Shugaban Faransa Francois Hollande yace za su yi kokarin gano gaskiyar abin da ya faru da Bafaranshen da Mayakan suka sace.

An sace Rodrigues ne a garin Kayes a ranar 20 ga watan Nuwamban 2012. Kuma Kungiyar MUJAO tana cikin Mayakan Jihadin da suka karbe ikon yankin arewacin Mali tare da mayakan Abzinawa kafin dakarun Faransa su kwato yankin a watan Janairun 2013.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.