Bom ya kashe babban Jami’in ‘Yan sanda a Masar
Jami’an tsaro a kasar Masar sun tabbatar da mutuwar wani Janar din ‘Yan Sanda sakamakon wani bom da aka dasa a motarsa a birnin al Kahira, wannan kuma shi ne karo na biyar da ake kai wa Manyan Jami'an ‘Yan sanda hare hare a babban birnin kasar.
Wallafawa ranar:
Irin wannan harin ne aka kai wa Ahamed Zak wani babban kwamandan Jami’an tsaro da ke sahun gaba wajen karya magoya bayan hambararren shugaban kasa Mohammed Morsi.
Wata kungiyar Mayakan Jihadi mai suna Ajnad Misr ta fito tana ikirarin daukar alhakin hare haren da aka kai wa Manyan Jami’an tsaro tare da yin gargadin ci gaba da kai hare haren domin daukar fansa akan magoya bayan Morsi da aka kashe.
Amma akwai wata kungiyar Mayakan Jihadi ta Ansar Beit al-Magdis da ta yi ikirarin kai wasu hare haren kan ‘Yan sanda hadi da harin da aka kai a mashigin Sinai.
Tuni Gwamnatin Masar ta haramta ayyukan kungiyar 'Yan uwa Musulmi ta hambararren shugaban kasa Mohammed Morsi tare da jefa ta cikin jerin kungiyoyin 'Yan ta'adda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu