Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Ana ci gaba da gwabza fada a Sudan ta Kudu

'Yan tawaye da dakarun Gwamnatin Sudan ta kudu na ci gaba da gwabza fada a gabacin Jonglei da yankin arewa maso gabacin Upper Nile. Amurka da Majalisar Dinkin Duniya sun zargi 'Yan tawaye da kisan daruruwan fararen hula.

Wani Dan tawayen Sudan ta Kudu ya rufe bakinsa da hanci a kusa da gawa kwance a harabar Masallaci a Bentiu
Wani Dan tawayen Sudan ta Kudu ya rufe bakinsa da hanci a kusa da gawa kwance a harabar Masallaci a Bentiu REUTERS/Emre Rende
Talla

Amma 'Yan tawayen sun yi watsi da zargin kisan fararen hula bayan dakarun Gwamnati sun karbe ikon garin Bentiu daga ikonsu.

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi bangarorin biyu da aikata kisan kiyashi bayan kwashe kwanaki biyu 'Yan tawayen suna kisan fararen hula a Masallatai da wauraren Ibadar Kiristoci da Asibiti da kan hanya.

Kokarin da kasashen gabacin Afrika ke yi na ganin an cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangaren Riek Machar da shugaban kasa Salva Kiir ya cutura.

Rikicin kasar ya tursasawa dubban mutane kauracewa gidajensu tun lokacin da rikicin ya barke a watan Disamban bara.

Rikicin kuma yanzu ya rikide ne tsakanin kabilar Dinka ta Salva Kiir da kabilar Neur ta Tsohon Mataimakin shugaban kasa Riek Machar .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.