Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan mata 234 ne suka rage hannun 'yan Boko Haram

Adadin dalibai matan da aka sace a garin Chibok na jihar Borno a Tarayyar Najeriya ya dada karuwa, inda yanzu haka ake cewa dalibai 234 aka yi garkuwa da su ba wai sama da 100 ba kamar yadda aka bayyana a baya.

Sojojin Najeriya suna binciken wani sansanin mayakan Boko Haram a Kirenowa
Sojojin Najeriya suna binciken wani sansanin mayakan Boko Haram a Kirenowa AFP Photo
Talla

Sabon adadin ya bayyana ne yayin da gwamnan Jihar Kashim Shetima tare da Sanata Ali Ndume suka ziyarci garin na Chibok domin mika wasu daga cikin yaran da suka gudu daga hannun wadanda suka kama su.

Sanata Ali Ndume ya shaida wa gidan rediyo Faransa cewa sun zanta da iyayen yaran da suka bata, kuma sun tabbatar masa da cewa akwai ‘yan mata 234 da har yanzu ba su dawo ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.