Najeriya: Jonathan bai gayyaci Gwamnonin APC ba a taron tsaro
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gudanar da taron gaggawa kan kokarin magance matsalar tsaro ba tare da Gwamnonin Jam’iyar APC mai adawa ba. Gwamnan Jahar Adamawa Murtala Nyanko yace sun kauracewa taron ne saboda ba a gayyace su ba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Taron wanda ya kunshi manyan Jami’an tsaro da Gwamnonin Jahohin kasar an gudanar da shi ne ba tare an bayyana matsayar da aka cim ma ba akan yadda za’a magance matsalar tsaron da ke addabar yankin arewaci.
Rahoton Kabir Yusuf daga Abuja
Wasu kafofin yada labarai a Najeriya sun ruwaito wani babban na hannun damar shugaba Jonathan yana tabbatar da cewea gangan gwamnatin PDP ta ki gayyatar Gwamnonin na APC.
Gwamnan Jahar Adamawa Murtala Nyako ya shaidawa RFI Hausa cewa bayan sun hallara zuwa Abuja daga baya aka shaida masu cewa an dage taron.
Jam’iyyar APC ce dai ke mulki a dukkanin Jahohi uku a yankin arewa maso gabaci da ke cikin dokar ta-baci da gwamnatin Jonathan ta kafa saboda kazancewar matsalar tsaro amma an gudanar da taron ne ba tare da wani daga cikinsu ba saboda wasu dalilai na siyasa.
Gwamnan Jahar Adamawa Murtala Nyako
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu