Isa ga babban shafi
Nijar

An dau hanyar tube kakakin Majalisar kasar Nijar

A wani abu da ake kallo da cewa yunkuri ne bangaren masu rinjaye ke yi domin tube shugaban Majalisar Dokokin Jamahuriyar Nijar Hama Amadou wanda ya fito daga bangaren adawa, wasu ‘yan majalisar kasar daga bangaren masu rinjaye, sun bukaci a canza dokokin cikin gida na Majalisar domin dawo da wa’adin shugabancinta zuwa shekara daya, a maimakon shekaru 5 da aka zabi Hama Amadou akai. Rikici tsakanin ‘yan adawa da masu rinjaye a jamhuriyar Nijar, ya kara tsananta ne bayan da jam’iyyar Moden Lumana Afirka ta shugaban Majalisar dokokin kasar Hama Amadou ta fice daga gwamnati tare da kulla kawance da ‘yan adawa a watannin da suka gabata, lamarin da ya sa aka kori dukkanin ministocin jam’iyyar da ke yi biyayya ga Hama Amadou daga gwamnati. 

Mahamadou Issoufou, shugaban jamhuriyar Nijar tareda Hama Amadou shugaban majalisar Dokokin
Mahamadou Issoufou, shugaban jamhuriyar Nijar tareda Hama Amadou shugaban majalisar Dokokin AFP / BOUREIMA HAMA
Talla

Tun daga wannan lokaci ne dai aka yi hasashen cewa kul bade magoya bayan shugaban kasar Issifou Mahamadou, za su yi yunkurin tube Hama Amadu daga kan mukaminsa,
inda a jiya Alhamis masu rinjayen suka bukaci a sauya dokokin cikin gida na majalisar wanda hakan zai bayar da damar sabunta wa’adin shugabanci majalisar a kowace shekara maimaikon shekaru 5 da ke cikin doka a halin yanzu.

To sai dai abin lura anan an zabi Hama Amadou ne a ranar 7 ga watan Afrilun shekara ta 2011 domin ya shugabanci majalisar akan wa’adi na tsawon shekaru 5 cur, yayin da na hannun damar shugaban kasar ke ganin cewa ba ta yadda za a bar dan adawa a kan wannann matsayi.

A daya bangare kuwa a zamanta na ranar Alhamis 17 ga watan Afrilu, majalisar ta sabunta wa’adin shugabancin uku daga cikin mataimakan shugaban majalisar guda 5 wanda a ka’ida ana yin haka ne a kowace shekara, yayin da 2 daga cikinsu wadanda suka fito daga bangaren adawa suka kasa samun kuri’un da ake bukata, duk da cewa kundin tsarin tafiyar da majalisar, ya ce kujerun biyu wani hakki ne na ‘yan adawa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.