Isa ga babban shafi
Senegal

Kotu ta ba da umurnin a ci gaba da tsare Karim Wade

Kotu a birnin Dakar dake Senegal ta bayar da umurnin ci gaba da tsare Karim Wade, dan tsohon shugaban kasar Abdoullaye, har nan da watanni biyu masu zuwa, inda ake tuhumar sa da yin facaka da kudaden gwamnati lokacin da yake rike da mukamin minista.

Dan tsohon Shugaban kasar Senegal Karim Wade
Dan tsohon Shugaban kasar Senegal Karim Wade REUTERS/Joe Penney/
Talla

A yau dai Karim Wade ya share tsawon shekara daya tsare a gidan yari, inda yake fuskantar zargin cin hanci da rashawa da kuma yin almundahna da kudaden gwamnati a lokacin da yake rike da mumakin minista karkashin gwamnatin mahaifinsa.

A ranar 17 ga watan Afrilun shekarar bara ne dai kotu ta bayar da umurnin tsare shi har na tsawon watanni shida, bisa zargin cewa ya karkata akalar kudaden da yawansu ya kai cefa biliyan 694 kwatankwacin Euro miliyan dubu daya.

Yayin da wata kotun ta bayar da umurnin tsare shi domin gudanar da bincike dangane da zargin yin almundahnar da ta kai ta cefa bilyan 98, wadanda aka ce ya boye a wani banki da ke tsibirin Monaco, yayin da aka ce ya mallaki wasu kudaden da yawansu ya kai cefa bilyan 45 a kasar Singapour.

Shi dai wanda ake tuhumar, mahaifinsa kuma tsohon shugaban kasa Abdullaye Wade ya danka masa ragamar jagoracin ma’aikatu biyar da suka hada da ta makamashi, gine-gine, zirga-zirgar jiragen sama sannan kuma maio bai wa shugaban kasar shawara na musamman duk a lokaci daya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.