Isa ga babban shafi
Najeriya

Babu tabbas ga makomar Matan da aka sace a Chibok

Bayanai da ke fitowa daga Najeriya masu karo da juna na nuna har yanzu babu tabbas ga makomar Matan da ‘Yan bindiga suka sace a garin Chibok da ke cikin Jahar Borno a yankin arewacin kasar. Rundunar Tsaron Najeriya tace ta kubutar da daliban mata 129 daga cikin wadanda aka sace amma wasu majiyoyi daga yankin sun karyata ikirarin.

Dakarun Sojin Najeriya da ke farautar Mayakan Boko Haram
Dakarun Sojin Najeriya da ke farautar Mayakan Boko Haram AFP/Quentin Leboucher
Talla

Kakakin rundunar Sojin ta Najeriya, Manjo Janar Chris Olukolade, ya shaidawa RFI Hausa cewa yanzu dalibai 8 suka rage ba’a gano ba, yayin da suka kama daya daga cikin wadanda suka sace su.

A cikin wata sanarwar shugaban makarantar daliban ya tabbatar da cewa dalibai 8 suka rage a kubutar daga cikin daliban da ‘Yan bindiga suka sace.

Shugaban Makarantar ya tabbatar wa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa cewa daliban sun tsere ne daga hannun ‘Yan bindigar da suka sace su.

Amma Gwamnan Jahar Borno Kashin Shettima ya shaidawa manema labarai cewa dalibai 14 suka tsere tare da yin alkawalin kudi Naira Miliyan 50 ga duk wanda ya taimaka aka kubutar da daliban sama da 100 da aka sace.

Wasu daga cikin Iyayen yaran da aka sace sun ce uku daga cikinsu ne suka tsere wadanda suka ce ‘Yan bindigan sun gudu da su ne zuwa dajin Sambisa a yankun Konduga daya daga cikin sansanin mayakan Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.